Bauchi: Gwamnati Ta Karbi Rigakafin Korona

Kimanin magungunan rigakafin Mashakon Numfashi da akafi sani da suna (Korona Bairos) guda dubu 80,570 daga cikin dubu 150,000 wanda gwamnatin Jihar Bauchi ta karba don raba ma al’umma daga hukumar kiwon lafiya ta kasa a matakin farko.

Mataimakin Gwamnan Jihar ne Sanata Baba Tela, ya fada ma manema labarai hakan, jim kadan bayan ya marabci maganin rigakafin, yau da sanyi safiyar Laraba, a dakin ajiye magani a Asibitin koyarwa na tunawa da Abubakar Tafawa Balewa (ATBUTH) dake Bauchin.

Baba Tela yace ana sa ran fara bada rigakafin ne ga ma’aikatan kiwon lafiya, da Jami’an Gwamnati, shuwagabbanin gargajiya dana addinai, kana yaku bayi su biyo baya.

Mataimakin Gwamnan wanda dama shine Shugaban kwamitin kula da hidimar cutar annobar Korona, dana zazzabin beraye a Jihar Bauchin, inda yace ranar Alhamis ne za’a fara bada rigakafin

Kana ya kara da cewa, maganin rigakafin za a kaishe sassan kananan hukimomi 20 da kuma gundumomi 323 da suke fadin jihar, kana a baiwa yara da tsofaffin masu shekarun da ya shura

Baba Tela ya bada tabbacin cewa za a raba maganin ya yadda ya dace da tsari, san nan ya kirayi al’ummar Jihar dasu karbi wannan maganin rigakafin da hannu biyu, kar suji tsoron komai, domin asamu a kaucewa ci gaba da yaduwar annobar a cikin Jama’a

Bugu da kari tun a farko
Shugaba kiwon.lafiya a matakin farko na Jihar Dakta Rilwanu Mohammed, lokacin da suka karbi magungunan a cikin dare ne shiya sa suka Isa dashi kai tsaye zuwa wajen ajiye magani na Asibitin koyarwan, a daren jiya kamar yadda hukumar lafiya ta kasa ta bada ummurni.

Rilwanu Mohammed ya kara da cewa, dole ne ayi maza maza a kaisu wuraren bada riga kafin, don gujewa lalacewa

Daga karshe ya jaddada aniyar gwamnatin Jihar da cewa kowa zai samu wan nan rigakafin mahanin cikin sauki, don rage yaduwar chutar a dukkanin fadin Jihar.

Daga Adamu Shehu Bauchi

Labarai Makamanta