Bauchi: Gwamna Da Uwargidansa Sun Karbi Rigakafin Korona

Gwamnan Jihar Bauchi Bala Mohammed tare da Uwargidansa Hajiya Aisha Bala Mohammed, sun karbi allurar rigakafin cutar Korona tare da sauran makarraban gwamnati da masu sarautun gargajiya da limamai dana Massallatai da Chochi-Chochi, a fadin Jihar baki daya.

Tarun kaddamar da fara rigakafin ya samu hallartar mataimakin Gwamnan Jihar, Sanata Baba Tela, da jama a da dama cikin su harda yan’jaridu masu dauko rahotanni daga sassan fadin Jihar, wanda ya gudana a dakin taro na gidan gwamnatin Jihar

Da yake jawabinsa jim kadan bayan kaddamar da aikin rigakafin da kuma zama na farko a Jihar da aka yima allurar rigakafin, gwamna Bala Mohammed, yace tabbas rigakafin zaiyi sanadiyyar kawo karshen wan anan annoba ta Korona.

Kana ya bayyana farin cikinsa da ganin yadda malamai na addinai biyu suka rungumi shirin karbar allurar rigakafin, yace su ci gaba da fadakar da al’ummarsu kan alfanun allurar rigakafin.

Gwamna Bala ya sake cewa yawan allurar rigakafin 150,000 yayi ma Jihar Bauchi kadan, da annan ya roki gwamnatin tarayya data sayo ma Yan Najeriya iya wadda zai wadaci kasan

“Nayi farin ciki da wan nan rana, wanda shine kusan shirin da zai kawo karshen wan nan cuta baki daya, inda nine na fara kamuwa da ita da kuma mataimakina da wasu Jami’an gwamnatin,a Jihar man, yau gashi muna karbar allurar rigakafin wan nan cuta, yayin da wasu masana na duniya suka gano maganin”

Yace “ina mai tabbatar maku da bayan munkarbi allurar to ba shikenan ba, zamu ci gaba da sanya amawalin baki da hanci nan, domin ganin mun yaki cutar gaba daya”

Bugu da kari Gwamnan yayi ma.kowa godiya ta mussaman kan wan nan muhimmin aiki na shawo kan cutar, duk da mastalolin da aka ci karo dasu, ya godewa abikan hudda na kasa dama na ketare Hukumar kiwon lafiya ta duniya (WHO) da suke ta kaiwa da komowa don ganin ancimma nasarar kawar da wan nan annoba ta Korona a Jihar Bauchi, da ma Najeriya baki daya.

Daga karshe yace ya godewa Mai taimakin Gwamnan Jihar da suaran jam’ian kiwon lafiya na Jihar da kwamitocinda sukayi aiki kafada da kafada, har izuwa wan nan lokaci,

Daga Adamu Shehu Bauchi

Labarai Makamanta