Bauchi: Gwamna Bala Ya Yi Kira Ga Shugabannin Kananan Hukumomi Da Tsuke Bakin Aljihu

Daga Adamu Shehu Bauchi

Gwamnan Jihar Bauchi Bala Abdulkadir Mohammed ya umarci Shuwagabbanin kananan hukumomi da su rage kashe kudade ta wasu hanyoyin da bazai taimaki al’ummar da suke karkashinsu ba, ko kuma su fuskanci kiyayya daga talakawan dake kusa daku.

Gwamnan yayi wan nan furucin ne yayin wani zama na musamman da yayi da Shuwagabbanin kananan hokumomi ashirin 20 na jihar, don tattaunawa kan shirin basu kodaden su domin suci gashin kansu da aka jima ana ta kiki-kaka, da kai ruwa rana a kan batun.

Bala ya ce Gwamnati zata basu gashin kansu, amma bisa alkawarin dole su tashi tsaye suyi ma mutanen su aiki tukuru da dogaro da kansu a matsayin kananan hukumomi, wadda dokan kasa ta basu, yace saboda haka dole su zama masu taka tsantsan kan kudaden al’umma da za’a sake mika masu kai tsaye.

Yace dole ne Shuwagabbanin kananan hukumomi su iya Tsuke bakin aljihu, suyi amfani da kadan da yazo masu, kuma su fitar da hanyoyin samun kudaden shiga domin gwamnatin Jihar ta gaji da biyan su albashi da wasu sauran ayyukan more rayuwa.

“Mun fahimci baku da zimman iya cin gashin kanku da muke kokarin baku, kawai kuna da Ido ne akan kudaden, bawai aikin da zakuyi ma al’umma ba, kina ganin yadda muka bude ayyuka da dan abin da ke hannun mu, wanda bai taka kara ya karya ba” Inji Gwamna.

Daga yanzu ina so ku fara biyan kanku albashin ma’aikatan kana nan hukumomi, na gaji da biyan ku ta cikin asusun jihar Bauchi, ga shi dama ana korafin ma’aikata na boge, ku sani yanzu zaku rika daukan nauyin kanku”

Abunda baku sani ba, muna kara ma wasu kananan hukumomi, amma wadansu nasu ya ishesu, duk da haka baza musa ido muna karbowa kana nan hukumomi suna karbe wa ba!” Ya jaddada.

Daga karshe Bala, ya ce in akayi la’akari da kudaden da ake kashewa wajen salary kimanin naira miliyan dari biyar 500 a wata daya hakan bazai yiwu ba.

Yace naira miliyan Taltin 30 kadai ba zai Isa a biya albashi karamar hukumar Toro ba, saboda akwa wadanda suka mutu, ga Kuma wadanda suke Abuja suna karbar albashi ku kun sansu, dole ne a dakata biya daga asusun Jihar haka.

Labarai Makamanta