Bauchi: Gwamna Bala Ya Dakatar Da Shugabar Hukumar Marasa Galihu

Daga Adamu Shehu Bauchi

Gwamnan Bala Mohammed ya dakatar da shugabar hukumar kula da marayu da marasa galihu na Jihar Bauchi, Hassana Arkila akan zargin al’mundahana tare da sama da fadi

Sanarwar ta fito ne daga fadar gwamnatin tare da sa hannun mai bawa Gwamna shawara ta fanin yada labarai Kwamred Mukhtar Gidado, kuma aka tura ma manema labarai

Gwamnan nan take ya kafa kwamiti na musamman domin binciken zarge-zargen da ake ma hukumar karkashin jagorancin ita Hasana Arkila na badakala a hukumar.

Sanarwar tace gwmana Bala ya ce, dakatarwar ta fara aiki ne nan take ba tare da wani bata lokaci ba.

Har’ila yau, an umarchi Shugaban hukumar data ajiye aikin ta nan take ta tattara dukkan komai na jagorancin hukumar ta baiwa Wanda yafi kowa mukami a hukumar.

Sa’anan sanarwar tace yin hakan shine zai bama kwamitin binciken zarafin aiwatar da aikin da aka sasu nan take ba tare da shakku ba

Ita wan nan hukumar dai wacce aka fi sani da suna (BASOVCA) a turance, an kirkiro ta ne domin tallafa ma marasa galihu da kuma marayu da masu rauni ta fuskar rayuwa a cikin al’umma, don a taimaka masu suma suyi rayuwa kamar sauran al’umma.

Cikin ayyukan wan nan hukumar akwai tallafi na karatun marayu da marasa galihu har zuwa girmansu, da koyon sana’oi na dogaro da kai da, wanda karshe ake yaye su domin su amfani kansu da kuma al’umma baki daya.

Labarai Makamanta