Bauchi: Dan Majalisar Tarayya Ya Bada Tallafin Kayayyakin Lafiya

Daga Adamu Shehu Bauchi

Dan’majalisar tarayya dake wakiltar mazabar Darazo/Ganjuwa Alhaji Mansur Manu Soro ya bayar da naira Miliyan bakwai na tallafi ga mata da matasa da Kuma motocin daukan marasa lafiya da gina asibitin shan magani da kayan aiki a wadanan mazabu guda biyu a Jihar Bauchi.

Yayin da yake jawabin sa Dan’majalisar tarayya a wajen taron da ya gudana a jamiar Jihar Bauchi dake garin Yuli, suna aiki kafada da kafada da gwamnatin Jihar Bauchi ta wajen ayyukan ci gaban al’umma, a Jihar baki daya musamman a yankin da yake wakiltar majalisar tarayya, yace suna godiya da hadin kai da Gwamna ke bayarwa a cigaban jihar.

Ya kara da cewa wadan nan tallafi da kayan asibiti da makaranti da kuma wadansu ayyukan more rayuwa a cikin al’umma, musamman ga marasa galihu da masu rauni sosai a yan’kunan Jihar Bauchi

Kana Manu Soro yace, yayi ma wadan nan asibitocin shan magani guda hudu da makaranti guda hudu sunayen mata fitattu a cikin jiha da Najeriya, a kauyukan Darazo da Ganjuwa domin ci gaban al’ummar yan’kinsu da Jihar Bauchi baki daya.

Sauran kayayyakin tallafinnsunnhada da wayar hannu 441 ga matan yan’kunan Darazo da Ganjuwa da Kuma koyar dasu ayyukan unguwan zoma domin taimakawa malaman asibiti a yankin don a samu ragiwar mutuwar masu juna biyu a yan’kunan da yake wakilta.

A jawabin sa Gwamnan jihar Bauchi Bala Abdulkadir Mohammed yace ya zama dole su hada hannu da karfi waje daya domin ciyar da al’ummar Jihar Bauchi.

Yace gwamnatinsu tana alfahari da Manu Soro da irin ayyukan more rayuwa, da ya kawo a Jihar, duk da cewa basu fito a jamiyya daya ba, yace yanzu shugabanci suke ma al’ummar jiha ba siyasa ba, mu muna PDP shi kuma suna APC.

Bala yace tunda suka shigo a gwamnatance sunyi ayyuka iri dabam dabam na more rayuwan al’umman jihar Bauchi a cikin birni da kauyuka

“Yau mun taru anan don kaddamar da ayyukan da dan’majalisa Manu Soro ya aiwatar a mazabarsa da yake wakilta a majalisar kasa ta tarayya Darazo/Ganjuwa” Gwamna ya fada.

Gwamna Bala ya kara da cewa Dan’majalisar da daukannirin wadan nan ayyuka abun ayaba ne matuka gaya.
Kana ya kalubalanci sauran Yan’ majalisar tarayya da su zo su cire son zuciya suyi ma mutane aiki tare da hadin gwiwa, da Gwamnati ba su tafi suna neman raba kawunan jama’a ba ko al’umma don siyasa irin ta son kai da rashin lisaffi.

Labarai Makamanta