Bauchi: Dalibai Sun Yi Allah Wadai Da Tabarbarewar Ilimi

Daga Adamu Shehu Bauchi

Gungun daliban Jihar Bauchi sunyi Allah wadai da yadda harkokin Ilimi ya tabarbare a cikin kankanin lokaci, ta wajen rashin tallafi na makaranta da ake bawa kowani dalibi dan asalin Jihar daga cikin asusun gwamnatin da Kuma na karo ilimin a kasashen ketare

Shugaban Gungun daliban Kum mai magana da ywun ta Aliyu Hussaini shine ya fadi hakan a lokacin da yake zan’tawa da manema labarai a sakatariyar Yan’jarida reshen jihar Bauchi

Shugaban nasu yace an kirkiro Gungun daliban me da nufin gano matsalolin dake addaban dalibai Yan’salin jihar Bauchi, ko zasu lalubu bakin zaren da hadin gwiwa da kwararru ta fannin Ilimin a bangarori da dama

A cewarsu a karkashin gwamnatin da ta shude daliban Jihar sunyi walwala Kuma aan bunkasa harkar Ilimi sosai , ta hanyar kirkiro sabbin dabaru na koyarwa, yace a cikinsu akwai Makarantu na musamman ga daliban Jihar, tallafin karatu na cikin gida da Kuma na kasashen ketare, da dai sauransu.

Aliyu yaci gabanda cewa,” karkashin wan nan Gwamnati mai chi a yanzu, an samu Kuma baya da bazai misaltu ba, har takai babu dalibi dan jihar Bauchi Daya karbi tallafin karatu na kasashen ketare, domin sun rufe bayarwa tun hawansu karagar mulki, na cikin gidan ma sai shafaffu da mai ake baiwa, saidai watakila in lokacin zabe yazu zasu bayar”. ya fada.

Bugu da kari yace ” Kudin tallafi na dalibai masu karatu ta fannin kiwon lafiya da tsohowar gwamnatin Jihar take badawa suma yanzu ba a basu tallafin, duk da muhimmancin bangaren kiwon lafiya, abun ya zama tarihi a yanzu” Inji Kakakin su.

Har ila yau, ya kara da cewa “yanzu baza muyi shiru mu zuba ma Gwamnati Ido ba mungaji da lallabawa abun ya ishe mu haka, mumankira da babban mirya idanngwamnati Mai chi ta gaza tu, su shirya zabe na nan tafe akwai dantakarar da yake tallafama daliban Jihar Bauchi, AirMashal Sadiq Abaubakar sabo da haka, zamu sauya akalar mu a zaben 2023 a Jihar Bauchi”. Aliyu Hussain ya jaddada.

Labarai Makamanta