Bauchi: An Yi Kiran Dawowa Sarakuna Martabarsu A Dokar Kasa

Mai martaba Sarkin Bauchi Dokta Rilwanu Sulaiman Adamu yaja hankalin yan’majalisun jihohi da suci gaba da aiki tukuru don ganin an dawo ma da sarakunan gargajiya Martabarsu a cikin tsarin dokar kasan Najeriya.

Sarkin yayi wan nan kira ne a lokacin da kakakin yan’majalisu na jihohi 36 suka kai mashi gaisuwar bangirma a fadarsa Jim kadan bayan sun kammala taronsu a garin Bauchi a kwana nan

Dokta Rilwanu Sulaiman yace su ba Yan siyasa bane amma suna da daraja a cikin al’umma ya kamata ace ana mutunta su a ciki kundin tsarin mulkin Najeriya da aka sansu tun fil azal, kana yace sarakunan gargajiya suna taka rawa sosai ta wajen kawo zaman lafiya, saboda haka ya kamata a shigar dasu cikin tsari dokokim kasa,

Mai martaban ya sake cewa yasan Yan’majalisun suna kokari tunda akwai wan nan batu yanzu haka dake wanzuwa a tsakanin majalosun yace yana Mai basu karfin gwiwa domin samun mafiya rinjaye kan wan nan batu.

Bugu da kari ya kirayi Yan siyasa da suyi koyi da yan’majalisar dokokin Jihar Bauchi kan gudanar da sha’anin mulkin majalisa yace duk da ba jam’iyya daya suka fito da Gwamnan jihar ba amma kansu yana hade.

Shugaban tawagar Yan’majalisun jihohin Kuma kakakin majalisar Jihar Bauchi Abubakar Y. Sulaiman yace sunzo fadar mai martaba ne domin neman addu’a irin na iyayen kasa,

Da kuma jaddadamasa goyon baya kan irin gudumuwar masu rike da sarautun gargajiya suke badawa ta wajen kwantar da hankalin mutane a zauna lafiya, banda tashin hankali, da ka iya kawo rashin ci gaba.

Kakakin yayi nuni da cewa zasu tabbatar da ganin duk wata doka da zata kawo ci gaban Al’umman Najeriya ba ayi mata kafar ungulu ba, don haka suna sane da muhimmancin sarakunan gargajiya.

Daga karshe Yan’majalisun sun zagaya don gane ma idanunsu wasu ayyukan da gwamnatin Jihar take aiwatarwa a fadin Jihar baki daya don tabbatar da abunda akasa a gaba anayinsa ko akasin haka a matsayin su na wakilan al’umma.
#

Labarai Makamanta