Bauchi: An Sanya Wa Jami’ar Jihar Sunan Sa’adu Zungur


Majalisar zartarwa ta jihar Bauchi ta amince da sauya sunan jami’ar jihar Bauchi, Daga Bauchi state University Gadau zuwa jami’ar Sa’adu Zungur.


An yi wannan ne don kara daga kima da martaban Marigayi Malam Saadu Zungur wanda yaba da Cikekkiyyar Gudummawa a fannin ilimi kuma yana cikin shugabannin da suka yi gwagwarmayar neman ’yanci ma Kasar mu Nijeriya tare da su malamin Malam Aminu Kano, wanda ya taɓa zama sakataren NCNC.


Ɗan gwagwarmayar siyasa ne sosai kuma dan kishin ci gaban Arewa da kare al’adun mu shi fitila ne a fagen siyasar Arewa har zuwa yau.


Kuma ya kasance babban mawaƙin hausa kuma mai wakokin karfafa cigaba da kuma zamantakewa.


Gwamna, Sanata Bala Abdulkadir Mohammed, take yayi na’am da wannan sauyi domin martaba darajan malam Sa’adu Zungur.

Kwamishinan ilimi na jihar Bauchi Dr Aliyu Usman Tilde yace – :
Wannan babbar rana ce a tarihin ilimi a jihar Bauchi.
Dr. Aliyu U. Tilde
Kwamishina
Ma’aikatar Ilimi na
Bauchi
10 ga Fabrairu 2021 .

Labarai Makamanta