Bauchi: An Sallami Malamai Biyu Sakamakon Lalata Da Dalibai

Daga Adamu Shehu Bauchi

Makarantar Kimiya da Fasaha ta gwamnatin tarayya dake Jihar Bauchi ta sallame Malamai biyu daga aiki nan take biyo bayan rahoton kwamitin da makarantan ta kafa don binciko zargin da akayi masu kan lalatar, da Yan’mata dalibai su biyu.

Da yake ma manema labarai karin haske a yau Lahadi a babban dakin taro na shuwagabannin hukumar gudanar da al’amurran ci gaban makarantar, Barista Isaac Ogbobula, tare da shugaban makarantar baki daya Akitek Sanusi Waziri Gumau sunyi bayanin yadda kwamitin suka kawo rahoton tare da bin kwakwafin sahihancin binciken da akayi, kana sun gano cewa lallai wadanda ake zargin sun aikata wan nan laifi.

Kana suka ce aikata wan nan danyen laifin bisa ga rahoton kwamitin aikata laifin lalata da daliban mata biyu a makarantar ya saba ma dokokin makarantar.

Har ila’yau basuyi wata wata ba suka cimma matsaya kuma suka zartar da hukunci akan wadan nan malaimai guda biyu Malam Adebusoye Micheal Sunday na bangaren koyar da ilimin kayan abinci masu gina jiki, kayan marmari da danginsu da Kuma Malam Musa Baba Abubakar na ban garen koyar da ilimin bai daya Suka ce dukkansu an kore su daga aikin koyarwa a makarantar har abada.

Yace jan’ kafa da suka yi wajen yanke wan nan hukunci ba da gangan bane sunbi abin ne sau fa kafa, “bamu da wani abu da muke boyewa, muna bin diddigi ne kadai, dan gane da dokan makarantan ne ya kawo jinkiri, nayi mamakin yadda wasu kafafen watsa labarai suke cewa munyi biris da maganan, ko kadan” inji Sunusi Gumau

“Tunda muka samunrahoton abun nan da ya faru ba muyi kasa a gwiwa ba maku nada kwamiti dabam-dabam nan take, Kuma gashi mun sami sakamakon binciken” inji Shugaban Makarantar.

Daga karshe Shugaban Makarantar Sunusi Gumau, yace a yanzu haka an sallame dalibai talatin daga makarantar kannaikata laifuffuka dabam dabam, t wajennzana jarabawa da dai sauransu

Labarai Makamanta