Bauchi: An Damke Wadanda Suka Kashe ‘Yar Shekara 5 Da Cusa Gawarta A Buhu

Daga Adamu Shehu Bauchi

Rundunar Jami’an Tsaro da akafi sani da suna (Civil Defence) sun samu nasarar cafke mutum biyu wadanda ake zargin sun sace wata yarinya mai suna Kadijah Abdullahi ‘yar shekara biyar suka kashe ta suka cusa ta a buhu suka rufe a wani kangon kicin dake wani gida a unguwan kauyen na Rabi dake a karamar hukumar Toro Jihar Bauchi.

Shugaban rundunar na jihar Nurudden Abdullahi da yake zantawa da manema labarai a Shalkwatar rundunar dake Bauchi, yace bayan samun labarin ta’asar Jami’an tsaro suka shiga aikinsu inda suka gano waɗanda suka yi aika aikar.

Ya ƙara da cewa sun nemi kudin fansa daga Baban yarinyar mai suna Abdullahi Yusuf anan garin Narabin kusa da kan hanyar zuwa Jos daga Bauchi.

Har ila yau yace sun gano cewa Khadijah an kasheta ne a ranar 27 ga watan Afrilun 2022 bayan sun kai gawar zuwa babban asibitin Toro inda Likitoci suka tabbatar masu da mutuwar Khadijah.

Tun a farko Shugaban ya shaidama manema labarai cewa sunyi sa’insa da mahaifin Khadijah kan nawa za’a biya su kafin su saketa, inda daga karshe suka yadda a kaimusu Naira dubu dari da hamsin N150,500, Baban ya kai musu a cikin dajin kauyen Narabi a gindin wata bishiyar tsamiya, a cewar sa ko kafin iyayen Khadijah su kai kudin sun riga sun kashe Khadija sun sata a cikin buhu sun binne ta.

Da yake mayar da jawabi a shalkwatar (Civil defence) Abdullahi Yusuf mahaifin Khadijah cikin hawaye, Yana cewa makwabcinsa ne da ya yadda da dashi yayi mashi wannan cin amanan, “Ranar da zasu tashi a unguwarmu sai da nasa aka dafa musu abinci sukaci suka koshi har suka tafi da saura suna ta wasa da yarana a cikin gida, ashe ban san nufinsu ba.

Daga karashe ya nemi Gwamnati da ta bi masa haƙƙinsa domin hukuntasu daidai da abinda suka aikata ma ‘yarshi Khaadija wacce ake kira da Ilham,

Labarai Makamanta