Bauchi: Aljannu Ke Haddasa Haddura A Titunan Jihar – Hukumar Kiyaye Hadura

Rahotanni daga Jihar Bauchi na bayyana cewar Kwamandan hukumar kiyaye hadurra ta kasa (FRSC) dake Jihar Yusuf Abdullahi, ya koka kan yadda aka samun yawaitar hadurran mota a jihar a cikin watan Nuwamba na wannan shekarar.

Ya ce a cikin watan da ya gabata, mutane a kalla 35 ne suka mutu a wasu hadurran mota a fadin jihar, yayin da dama suka samu muguwar naƙasa.

Kwamandan ya bayyana damuwarsa kan lamarin inda ya bayyana cewa: “Shaidanun aljanu sun mamaye hanyoyin Bauchi a ‘yan kwanakin nan.”

Kwamanda Abdullahi, wanda ke jawabi ga mambobin kungiyar na musamman a ranar Asabar, 4 ga watan Disamba ya ce: “Ina baku hakurin fada muku, amma gaskiyar magana ita ce shaidanun aljannu sun mamaye hanyoyinmu a jihar Bauchi.

Lallai muna bukatar mu tashi tsaye mu yi wani abu don kwato hanyoyin. “Al’amarin ya yi muni sosai, a cikin watan Nuwamba; lamari ne da ake samun mace-mace a kowace rana domin ba a kasa samun mutuwar mutane 35 ba sakamakon hadurra a fadin jihar.

Wannan abin damuwa ne kuma abin tada hankali, dole ne a yi wani abu da sauri.” A cewarsa: “A kan hanyar Bauchi zuwa Kano, mun samu hadurran da suka yi sanadiyar mutuwar mutane sama da 15.

“A kan babbar hanyar Bauchi zuwa Jos, wasu motoci sun yi karo da manyan motocin tafiye-tafiye da suka yi sanadiyyar mutuwar mutane akalla 15 tare da kone wasu daga cikinsu kurmus.”

Labarai Makamanta