Bashi Na Dab Da Durkusar Da Najeriya – Sanusi

Tsigaggen Sarkin Kano kuma Tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya Sanusi, ya bayyana cewa tulin basussukan da Najeriya ta ciwo a kasashen waje idan aka kwatanta da 2011 zuwa 2021, to ya rubanya yawan kudin shigar da Najeriya ta samu sau 400.

Sanusi, wanda shi ne Sarkin Kano mai murabus, ya nuna tsananin damuwa kan irin gudun famfalakin ciwo bashin da Najeriya ke yi, wanda ya ce abin ya yi munin da zai iya jefa kasar a cikin ramin da samun wanda zai iya ceto ta, sai an sha wahalar sosai.

A ranar Alhamis ce Sanusi ya nuna wannan damuwar a wani taron-taron-daga-gida na ‘onlline’, da aka shirya kan matsalar da tattalin arzikin Najeriya ta shiga, da yake batun nema da rokon a yafe wa kasar wasu basussukan da su ka hana tattalin arzikin kasar farfadowa.

Gidauniyar Heinrich Böll Foundation ce ta shirya taron, inda a karin hasken da Sanusi ya yi, ya kara da cewa ana ta maganar cewa Najeriya na da karfin arzikin biyan bashi, amma an manta da wani muhimmin abu dangane da matsala ta biyan bashi.

“Idan ka shiga ka yi nazarin rahoton da mujallar Babban Bankin Najeriya (CBN) ya wallafa cikin 2011, za ka ga cewa gwamnatin tarayya ta samu kudaden shiga daga kowane bangarorin karbar harajin ta na tarayya, har tsabar kudi naira tiriliyan 18.9 a kan dala 1 na adadin naira 165. Wato kenan kudin shigar da gwamnatin tarayya ta tara a 2011 ya kai dala biliyan 55.5 a kan dala 1 naira 165.

“To amma bashi a lokacin bai wuce dala biliyan 5 ba. Sai dai zuwa shekarar 2020 bashin kasashen waje ya kai dala biliyan 33.4, sannan kuma kudin shiga bai wuce dala biliyan 8.3 ba.

“Kenan tulin bashi a ma’aunin kudaden shiga ya tashi daga kashi 8% bisa 100%, ya koma kashi 400% bisa tsakanin 2011 da 2020.

“Wannan kuwa wani gagarimar guguwar matsalar tattalin arziki ce wadda idan ta tirnike nan gaba, ba a san yadda za a iya kwantar da ita ba.

“Abin takaici kuma har yau Najeriya da kudaden fetur ta dogara wajen samun kudaden shiga. An kasa fadada tunanin kirkiro hanyoin da kasar za ta rika samun kudaden shiga baya ga danyen man fetur.”

Sanusi ya yi wannan bayani dalla-dalla na matsalar da ta dabaibaye Najeriya kan kudaden bashin da ake bin kasar, kuma ake ci gaba da falfala gudun famfalakin ciwowa. Sannan kuma a gefe daya ga matsalar karancin kudaden shiga da ake fama da su daga danyen man fetur din da ake takama da shi.

Labarai Makamanta