Barazanar Yunwa: Najeriya Za Ta Fito Da Shirin “Ciyar Da Kanka”

Rahotanni daga Abuja babban birnin tarayyar Najeriya na bayyana cewar a wani bangare na magance matsalar yunwa dake barazana ga kasar, gwamnatin tarayya karkashin jagorancin Shugaba Muhammadu Buhari na tunanin bullo da wani shiri na ciyar da kai, da ta kira ‘Operation Feed Yourself’ a turance.

A cewar mataimakin Shugaban kasa Yemi Osinbajo, shirin na da zimmar karfafa wa manoman zamani da na kauyuka samar da abinci wadatacce ga al’umma.

Mr Osinbajo ya yi jawabinsa a wani taro kan ”ingantaccen tsarin abinci” da aka yi a Abuja, wanda ya samu halartar mataimakiyar sakataren Majalisar Dinkin Duniya Amina Mohammed, da wasu gwamnonin jihohi da sauran masu ruwa da tsaki.

An yi hasashen cewa za a fuskanci karanci da kuma tsadar abinci a Najeriya a 2022.

Amma a cewar mataimakin shugaban kasar, lokaci bai kure ba da za a yi amfani da shirin na ‘Operation Feed Yourself’ don hada hannu wurin ceto al’umma daga fadawa cikin yunwa.

Labarai Makamanta