Barazanar Kai Hari Abuja: Gargadin Kasashen Yamma Kuskure Ne – Fadar Shugaban Kasa

Gwamnatin tarayya ta bayyana gargadin baya-bayan nan da kasashen yamma suka yi na yiwuwar kai harin ta’addanci a Abuja da wasu sassan kasar da cewa abu ne da bai ”dace” ba kuma bai ”kamata” ba.

Mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkoki tsaro Babagana Monguno ya shaida wa manema labarai cewa ”batun barazanar kai harin” ba shi da wani tushe balle makama.

Manguno na jawabi ne bayan taron gaggawa na majalisar tsaron kasar wanda shugaba Muhammadu Buhari ya jagoranta ranar Litinin.

Mai ba shugaban kasar shawara kan sha’anin tsaron ya ce, an shawo kan matsalar tsaron birnin Abuja, don haka a yanzu birnin ba ya cikin wata barazanar tsaro.

Monguno ya ce ‘’bai kamata a saka ‘yan Najeriya cikin fargaba da tashin hankali ba” ya kara da cewa ”batun barazanar karya ce, kuma bai kamata wani ya rika tsorata mutane ba’.

Shi ma ministan harkokin waje Geofrey Onyeama ya ce gwamnati na aiki da takwarorinta na kasashen waje domin ingantuwar alaka tsakanin ‘yan kasashen wajen da na Najeriya, ba tare da wani firgici ko tsoro ba.

A makon da ya gabata ne dai kasashen yamma irinsu Amurka da Birtaniya da Canada da Australiya suka fitar da jerin gargadin cewar akwai yiyuwar kai harin ta’addanci a birnin Abuja da wasu sassa na kasar, tare da umartar ‘yan kasashensu da su tsayar da tafiye-tafiye zuwa birnin.

Labarai Makamanta