Barayi Sun Sace Gangar Mai Miliyan 17 A Najeriya

Wannan rahoton na zuwa ne a daidai lokacin da Najeriya ke fama da karancin man fetur a sassan kasar.

Wani sabon bincike da aka gudanar kan lamurran da ke wakana a fannin arzikin man Najeriya ya nuna cewar, an fitar da ganga sama da miliyan 17 na danyen mai daga kasar zuwa kasashen ketare ta barauniyar hanya, a tsakanin shekarar 2016 zuwa 2020.

Rahoton da Andrew Ogochukwu Onwudili, babban jami’i mai binciken kudi na Najeriya ya fitar, ya kiyasta cewar kwatankwacin kudin danyen man fetur din da a iya cewa an sace daga kasar ya kai Dala Tiriliyan 1 da biliyan 20, da miliyan 969 da dubu 281.

A cikin rahoton, an tuhumi Ofishin Akanta-Janar na gwamnatin Najeriya da laifin biyan sama da Naira biliyan 73 ga jami’an da suke tantance inganci da adadin albarkatun mai da isakar gas din da ake shirin fitar da su daga kasar.

Labarai Makamanta