Bani Da Ra’ayin Shiga Siyasa A Rayuwata – Sunusi

Khalifan darikar Tijjaniyya a Najeriya, Muhammadu Sanusi II, ya bayyana ra’ayinsa a kan siyasar kasar Sanusi II ya ce ko kadan bai da ra’ayin neman wani mukamin siyasa a kasar Sai dai tsohon Sarkin Kanon ya ce zai ci gaba da fadakar da mutane kan irin shugabannin da ya dace a zaba Shugaban kungiyar darikar Tijjaniyya a Najeriya, Mallam Muhammadu Sanusi II, ya bayyana cewa baya da muradin tsayawa takarar wata kujerar siyasa a kasar.

Tsohon Sarkin Kanon ya kuma jadadda cewa zai ci gaba da wayar da kan al’umma a kan irin shugabannin da ya kamata a zaba, Domin Samun maskahar rayuwa.

An tattaro cewa Sanusi ya fadi hakan ne a wani taron Mukaddimai da Shehunnai na darika na farko tun bayan nada shi a matsayin Khalifan kungiyar na kasa.

Ya kuma bayyana cewa wannan ra’ayi nasa ba yana nufin tsunduma kai a harkar siyasa ba ne. Ya ce: “Idan muna da waɗanda muka aminta muka ce za su yi wa al’umma aiki za su gyara ƙasar, sai a hadu wuri guda a taimaka musu, wannan ba tsunduma a harkar siyasa ba ne, aiki ne na gyaran ƙasa da al’umma.”

Ya ci gaba da cewa rashin aikata hakan na iya jefa al’umman Najeriya cikin babban haɗari da ƙalubale. Ya kuma ce wajibi sai an bayar da fifiko wajen samar da ilimi musamman ga kananan yara kafin a iya magance matsalolin da ƙasar ke ciki.

“Idan babu ilimin nan, yaran nan da muke ganinsu ba mu sa su a makaranta ba, yayan wadansu kabilu suna can suna makaranta, nan gaba wadan nan yaran sune za sukafa kamfanoni, yaranmu su zama leburorinsu.

Labarai Makamanta

Leave a Reply