Bani Da Hannu A Rikicin Cikin Gida Na PDP – Atiku

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, kuma tsohon ɗan takarar shugabancin kasa a jam’iyyar PDP ya yi kira ga shugabannin PDP da su haɗa kansu domin cigaban jam’iyyar da kasa baki ɗaya.

Atiku ya yi wannan kiran ne a wata sanarwa da kakakinsa, Paul Ibe, ya fitar ranar Alhamis a Abuja yayin da yake martani kan sabon rikicin cikin gida da ya kunno a jam’iyyar.

Atiku yace PDP ba zata yarda a raba ta a dai-dai lokacin da yan Najeriya ke Allah-Allah su samu canjin gwamnati. Atiku yace a matsayinta na jam’iyyar adawa ya kamata ta gaggauta nemo hanyar warware matsalar domin bai kamata a zuba wa jam’iyya mai mulki ido tana cin karenta babu babbaka ba.

Tsohon mataimakin shugaban kasan ya musanta zargin da ake masa cewa yana da hannu a wajen rura wutar rikicin dake faruwa a PDP. Atiku ya kara da cewa bada jimawa ba yana daga cikin waɗanda suka jagoranci sulhu a faɗin kasar nan kuma ya yi imanin ta wannan hanyar ne kaɗai komai zai dai-daita.

“Jam’iyyar PDP ta zarce bukatun mu na kai da kai, ya kamata mu kintsa kanmu kafin mu fara maganar muradin mu. Wajibi ne mu kula sosai domin kome muka yi jam’iyya mai mulki tana kallo.” “Ba zamu bari jam’iyya ɗaya ta cigaba da mulkin Najeriya ba domin hakan zai sa fatan mutane na samun canji a 2023 ya bi iska.”

Labarai Makamanta

Leave a Reply