Bangaren Shari’a Ba Zai Yi Wasa Wajen Yakar Rashawa Ba – Babban Alkali

Babban Alkalin Najeriya mai Shari’a Tanko Mohammed, ya sha alwashin cewa fannin shari’ar kasar nan ba zai huta ba har sai ya ga bayan matsalar nan dake ci wa Najeriya tuwo a kwarya ta rashawa.

Babban alkalin ya sanar da hakan ne a ranar Talata yayin taron ganin bayan rashawa a kasar wanda ya gudana a babban birnin tarayya Abuja.

Kamar yadda yace, tsakanin shekarar 2020/2021, an yi shari’ar da ta danganci rashawa 756 a kasar nan. Ya kara da cewa, daga watan Janairu zuwa Nuwamban shekarar nan, wadanda ake zargi 1,144 aka yanke wa hukunci kan laifukan rashawa da makamantansu wanda ya hada da kwace daruruwan miliyoyi, jiragen sama takwas, gidajen mai bakwai da sauransu.

Mohammed ya yi kira ga alkalai kan su cire tsoro ko wariya kuma su yi hukunci kamar yadda tsarin shari’a ya tanadar domin dawo da ƙasar kan saiti. Ya kara da cewa, dukkan kasar da ke son cigaba, dole ne fannin shari’arta ya zama mai zaman kansh kuma babu abinda ke iya girgiza shi tun daga kan kudi zuwa wasu abubuwa.

Babban alkalin ya yi kira ga alkalai da su tashi tsaye kan dukkan kalubalen tare da dawowa da ‘yan Najeriya kwarin guiwa da tabbacinsu a fannin shari’a.

Labarai Makamanta