Ban Yi Ritaya Daga Siyasa Ba – Osinbajo

Bayan rashin cikar burinsa na son gadar shugaban kasa Muhammadu Buhari a 2023, mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya ce zai ci gaba da kasancewa a cikin harkar siyasa.

Osinbajo ya kuma bayyana cewa zai ci gaba da fafutukar son ganin Najeriya ta inganta da dukkanin fannoni yadda zata zarce tsara.

Ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi ga wakilan kungiyar magoya bayansa na PYO a kasar waje a wani taro da suka yi ta yanar gizo.

“Ina da niyyar ci gaba da kasancewa a harkar siyasar kasarmu, saboda na yarda cewa idan Allah ya bamu wannan damar, Canji zai zo kuma za mu kawo sauyi na gaske. “Ya zama dole mu ci gaba da turawa.

Idan muka gaji sannan muka ce bari muga yadda abun zai kasance, zai kara komawa baya fiye da yadda muka fara.”

A lokacin da jam’iyyar APC ta gudanar da taronta na musamman don zabar dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar na zaben 2023 a Eagles Square Abuja, Osinbajo ne ya zo na uku. Ya biyo bayan tsohon gwamnan jihar Lagas, Bola Tinubu da tsohon ministan sufuri, Mista Rotimi Amaechi.

Labarai Makamanta