Ban Taba Samun Dubu 10 A Sana’ar Fim Ba – Ladin Cima

Fitacciyar ƴar wasan Hausa, wadda ke fitowa a matsayin uwa ko kuma kaka a masana’antar Kannywood wato Ladin Cima Haruna wadda aka fi sani da Tambaya, ta bayyana cewa ta soma harkar fim bayan rasuwar mijinta inda ta ce dama tun a baya tana da sha’awar fim din. Ta ce Kaduna suke zuwa su yi fim saboda a zamanin babu gidan talabijin a Kano.

Ladin Cima wadda ta bayyana haka a tattaunawa da gidan Rediyon BBC ta bayyana cewa ta soma fitowa a fim tun zamanin mulkin tsohon shugaban kasaYakubu Gowon.

A cewarta, a tsawon lokacin da ta ɗauka tana fim, ba ta yi fim din da za a ɗauko dubu ashirin ko talatin ko hamsin a bata ba inda ta ce ana biyanta daga dubu biyu zuwa dubu biyar idan ta yi fim.

Ta ce a zamanin, ba a biyansu kuɗi, amma saboda sha’awar fim ɗin, suna ƙagara ranar Juma’a ta zo su tafi yin fim ɗin idan sun kammala sai Lahadi su koma Kano.

Ta bayyana cewa ta yi aiki a asibiti kuma zamanin Kabiru Gaya na gwamnan Kano ne ya ɗauke su aikin asibiti amma a yanzu ta yi ritaya.

Labarai Makamanta