Ban Taɓa Ganin Mashiririciyar Gwamnati Irin Ta Buhari Ba – Mohammed

Tsohon dan majalisar tarayya a jamhuriya ta 2, Junaidu Muhammad ya bayyana cewa shekarunsa 70 a Duniya amma bai taba ganin gwamnatin da bata san aikinta ba irin wadda ke kan mulki a yanzu.

Yace yawancin Alkawuran da akawa mutane ba’a cikasu ba sannan ga son kai wajan Nadenaden mukamai ga kuma rashin tsaro da yawa Najeriyar katutu.

Ya bayyana hakane a hirar da yayi da Sunnews inda yace matsalolin da gwamnatin ta zo ta iske karuwa suka yi maimakon su ragu.

Ya kara da cewa tin yana da shekaru 10 ya fara sanin yanda siyasar Najeriya ke gudana kuma tun daga shekaru 50 da suka gabata zuwa yanzu bai tama ganin gwamnatin da bata da manufa ba sai wannan.

Da aka tambayeshi yanda za’a shawo kan wannan matsala yace muddin shuwagabanni basu san aikinsu ba kamar yanda ake dasu yanzu, da wuya a yi nasarar shawo kan wannan matsala.

Labarai Makamanta