Ban Taɓa Ganin Maƙaryaci Kamar Babangida Aliyu Ba – Jonathan

Tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya karyata tsohon gwamnan jihar Neja, Babangida Aliyu, da ya ce wai shi Jonathan din ya karya alkawadin da ya dauka wa gwamnonin Arewa shi ne ya sa ya fadi zabe a 2015.

Daya daga cikin tsoffin hadiman Jonathan, Reno Omokri, wanda shine ya sanya wa martanin Jonathan hannu, ya ce Babangida Aliyu na surutai ne kawai don a ruka yi da shi a siyasa amma shirgegen makaryaci ne.

” Babu wani yarjejeniya da aka yi da ni a baya da gwamnonin Arewa 19 kan takara da na yi. Ba a taba yin haka da ni ba. Amma yanzu Aliyu ya wage baki yana yanko karya kawai don ya samu madafa a siyasance.

” Sule Lamido da kansa ya fadi cewa ba a taba yin haka ba. Hasalu ma shine Aliyu ya tausa idan na gwaggwale wa Jonathan ido a wancan lokacin.

Haka shima gwamnan Filato, Simon Lalong ya karyata Aliyu, yana mai cewa ba a taba zama don amincewa da yarjejeniya irin haka ba.

Labarai Makamanta