Ban Shelanta Neman Mijin Aure Ba – Rahama Sadau

Fitacciyar jarumar fina-finai Hausa Jaruma Rahama Sadau ta fito fili ta musanta zantukan dake yawo a kafafen sada zumuntar zamani inda ake cewa wai tana neman mijin aure.

A farkon makon nan ne aka fara yada cewa jarumar tana neman miji da gaggawa domin tana son yin aure, saboda ta matsu da ta samu Miji domin ta rufawa kanta asiri.

A fusace jaruma Rahama Sadau ta je shafinta na Instagram inda ta musanta rahoton tare da yi wa masu yaɗa wannan farfagadar wankin babban bargo.

Jaruma Rahama Ibrahim Sadau ta sake wallafa sakon a shafinta na Facebook tare da rubutu mai musanta wallafar. Tace ba ita ta rubuta hakan ba. “Bogi Bogi Bogi… Ban ce ba, kuma ban taba wallafa abu makamancin haka ba. Bogi ne kuma ba zan lamunci wannan ba.”

A halin yanzu dai wannan wallafa ta sadau bata yi wa wasu daga cikin mabiyanta na kafafen sada zumuntar zamani dadi ba, wadanda dama tuni suka kullaceta kuma suke ganin laifinta na barin Kannywood ta koma Nollywood.

A yayin rubuta wannan rahoton, wallafarta ta Instagram ta samu sama da martani 10,000. Yayin da wasu suka aminta da wallafarta, wasu kuwa sun ga bata dace ba.

Jaruma Rahama Sadau ta yi kaurin suna wurin jama’a biyo bayan wasu ɗabiu da akasarin jama’a musamman Hausawa ke ganin sun yi hannun riga da addini da al’ada.

Labarai Makamanta