Ban San Komai Ba A Ɓatar Kuɗin Makamai – Buratai

Tsohon Babban Hafsan Sojojin Najeriya, Tukur Buratai ya bayyana cewa babu ruwan sa da harkallar Dala Biliyan daya da aka fidda don sayen makamai.

A wata takarda wadda lauyan sa, Osuagwu Ugochukwu, ya sa wa hannu, Buratai ya ce a iya sanin sa bai san da wata dala biliyan 1 da aka taba ba shi wai na makamai kuma tsoffin manyan hafsoshin Najeriya su ka yi awon gaba da su ba.

“ Mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro Mungono wanda aka danganta wannan kalamai da shi ya ce ba haka ya fadi ba. Saboda haka muna kira ga mutane su daina cewa wai su Buratai sun waske da kudin makamai.”

A karshe lauyan ya gargadi masu ci gaba da yayata wannan magana da babu gaskiya a cikin ta cewe kotu ce za ta raba su.

A ranar Talata ce kuma Kwamitin Binciken Salwantar Kudaden Makamai ya gayyaci Sufeton ‘Yan Sanda Kasa, dangane da da wannan badakala.

A baya jami’an gwamnatin PDP ce aka tasa a gaba. Yanzu kuma tun APC ba ta kammala wa’adin ta ba, ana neman tsayar mata da alkiyamar ta kafin saukar ta daga mulki.

Labarai Makamanta