Ban Kashe Ummita Ba – Dan Chanan Da Ake Zargi Da Kashe Budurwa A Kano

Dan Chanan nan da ake zargi da kisan tsohuwar budurwasa mai suna Ummukhulsum Sani Buhari, wadda aka fi sani da Ummita, a Jihar Kano da ke arewacin Najeriya ya musanta tuhumar da ake yi masa a gaban kotu.

Bayan karanto masa zargin a gaban Babbar Kotun Kano, Mista Geng Quangrong ya ce ba gaskiya ba ne.

Mista Guo Cunru, shi ne mutumin da ofishin jakadancin China a Najeriya ya turo don ya yi wa wanda ake zargin tafinta daga turancin Ingilishi zuwa harshen Chinanci.

Lauya mai gabatar da kara wanda kuma shi ne kwamishinan Shari’a na Kano, Musa Abdullahi-Lawan, ya bukaci kotun ta fara sauraren tuhumar da ake yi wa wanda ake zargin.

Alkalin babbar kotun Mai Shari’a Sanusi Ado-Ma’aji ya ɗage shari’ar zuwa ranar 16 ga Nuwamban 2022 don gabatar da shaidun da masu kara suka za su kawo.

Ana zargin Mista Geng da kutsa kai cikin ɗakin Ummita tare da caka mata wuƙa a gidansu da ke unguwar Jan-Bulo da ke birnin Kano a watan Satumba.

Labarai Makamanta