Ban Fahimci Aure Ba Sai Da Na Shiga Dakin Miji – Malala

Yar gwagwarmayar nan mai ikirarin kare hakkin yara mata yar kasar Pakistan, Malala Yousafzai wacce ta amarce a makon da ya gabata ta ce a baya bata fahimci aure ba sai yanzu da ta shiga ɗakin miji.

Yar gwagwarmayar dai a baya ta bayyana karara ba ta goyon bayan aure. A wata hira da mujallar Vogue a watan Yuli Malala ta jaddada cewa; “Har yanzu, na kasa gane dalilin da ya sa mutane ke yin aure.”

Ta cigaba da cewa “Idan kana son rayuwa tare da wani mutum, me ye dalilin da dole sai an yi a rubutu (aure), me ya sa ba za ku yi zamanku a matsayin abokan rayuwa ba? Kodayake a cewar ta “Mahaifiyata ta taba daka min tsawa, tare da cewa; kada ki sake fadar haka! Dole ne ki yi aure, aure abu ne mai ban sha’awa”.

Aikuwa a makon jiya sai ga labarin aurenta kwatsam inda labarin ya yi matukar kada wata guguwa a shafukn sada zumunta musamman Tiwita da Facebook, inda dubban mutane suka dinga tofa albarkacin bakunansu.

Sai dai a wata hira da wani dan jarida Andrew Marr, matashiyar mai shekara 24, Malala Yousafzai, ta bayyana cewa a baya ta yi wa aure mummunan fahimta, kamar yadda ta shaidawa mujallar Vogue ta Birtaniya.

A cewar ta ”Ba na adawa da aure, na dai damu ne da yadda ake yin auren, da abin da yara mata da aka yi wa aure cikin kankantar shekaru ke gani, da auren dole, da halin da suke fuskanta bayan mutuwar auren, da kuma rashin daidaito tsakanin miji da mata na matukar daga min hankali.

Sannan rawar da al’ada ke takawa kan matan da suka samu kansu a irin wannan halin ita ma abin dubawa ce.”

Matashiyar mai shekara 24, ta sanar da auren nata a shafinta na Tuwita, inda ta ce ita da iyalanta sun gudanar da dan karamin bikin auren a gidansu da ke birnin Birmingham a Birtaniya.

Ta shaida wa kusan masu bibiyarta a shafin kusan miliyan biyu cewa ”wannan rana ce mai cike da farin ciki a rayuwata,” inda ta bayyana sunan mijin nata Asser.

Mijinta Asser Mlik fitaccen dan wasan Kurket ne, wanda yake rike da mukamin babban Manajan hukumar Kurket ta Pakistan (PCB).

Labarai Makamanta