An ruwaito wata kafar yada labarai ta bayyana cewa babban bankin ya saki naira miliyan 500 na cikin sabbin takardun kudi domin bai wa dan takarar gwamna a jam’iyyar Labour a Legas, Mista Gbadebo Rhodes-Vivour nasara kan sauran manyan jam’iyyu biyu a zaben gwamnan da za a yi ranar Asabar mai zuwa.
Amma a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin, mukaddashin Daraktan Sadarwa na CBN, Isa Abdulmumin, ya ce Emefiele “bai taba ganawa ko ma magana da Mista Gbadebo Rhodes Vivour ba”.
Da yake ambato wasu majiyoyi da ba a bayyana sunayensu ba, rahoton ya yi zargin cewa bayanan da aka fitar na daga cikin gudunmawar da Emefiele ya bayar na karbe Legas daga hannun Tinubu yayin da zababben shugaban kasar ya yi nasara
A wata sanarwa da ta fito daga bakin mukaddashin daraktan yada labarai na babban bankin Najeriya, CBN Isa Abdulmumin, ya ja hankalin babban bankin Najeriyar akan wani labari da ke cewa gwamna Godwin Emefiele ya kaddamar da wani sabon shiri na yaki da Zababben shugaban kasa’.
Labarin da aka ambata a baya ya ce, ya ci gaba da zargin cewa Gwamnan na CBN ya bayar da wasu makudan kudade ga wani dan siyasa kafin zaben gwamna a ranar 18 ga Maris din shekarar 2023.
Abdulmumin ya bayyana labarin a matsayin karya da mugunta, I nda kuma ya kara da cewa, gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele, bai sani ba kuma bai taba ganawa ko ma magana da Mista Gbadebo Rhodes Vivour tare da shi ko ta hanyar wani wakili ba.
Ya nanata cewa Gwamnan CBN baya shiga harkokin siyasa.
Kazalika ya kara da cewa, duk wanda ya samu sabanin bayanan da ya yi da ke tabbatar da cewa Gwamnan ya aikata wannan zargi toh ya fito yayi cikakken bayani.
You must log in to post a comment.