Ban Da Alaka Da ‘Yan Ta’adda: Sakatare Da Direbana Duk Kiristoci Ne – Pantami

Ministan Harkokin Sadarwa Isa Ali Pantami yace bayanan da aka fitar yan kwanakin nan akan yana da alaka da Yan Taliban da Al-Qaeda ba gaskiya bane.

Ministan ya kara dacewa baya da wata rashin jituwa da Kiristoci, inda ya bayyana cewa Direban sa da Sakatare gami da Mai taimaka masa, Dukkanin su Kiristoci ne.

Pantami ya bayyana haka a wata zantawa da Jaridar Peoples Gazette tayi dashi a ranar Juma’ar nan data gabata.

Yace”Direba na sunan sa Mai Keffi wanda addinin kiristanci yake bi. kuma akwai Ms Nwosu wadda Sakatariya ta ce, gami da Dr Femi shima kiristane kuma shine mai taimaka man”.

“Inda bana son Kiristoci, kuma bana kallon su a matsayin Yan uwa da bazanyi aiki dasu na tsawon lokaci ba. Haka Zalika na dauki Kiristoci da dama aiki fiye da Musulmai a matsayin ma’aikata na, sabudda na yarda da kwarewa da cancanta, bawai kabilanci ko bangaranci ba”>Pantami

“Ina kara kin jinin ayyukan ta’addan ci, kuma bana tare dasu ko kadan. Domin na dade ina koyarwa akan zaman lafiya a Tsakanin Al’umma da Dukkanin addinai”>>inji Ministan

An dai ta ruwaito cewa Pantami ya kasance a cikin matsatsi da rashin jindadi akan zargin yana da alaka da kungiyoyin yan ta’adda, wanda yan Najeriya sukai ta kiran Shugaba Muhammadu Buhari daya sauke shi.

Labarai Makamanta