Ban Ci Sisi A Kudin Makamai Ba – Buratai

Tsohon babban hafsan sojin Najeriya, Laftanan Janar Tukur Buratai, ya karyata rahoton cewa ya ci kudin da aka bada don sayan makamai lokacin da yake jagorancin rundunar dakarun kasar, kamar yadda wasu ke yaɗawa.

Janar Buratai wanda yayi murabus a makwannin baya, ya bayyana hakan ta bakin lauyansa, Osuagwu Ugochukwu, ranar Juma’a.

Mai ba shugaban kasa shawara kan lamarin tsaro, Babagana Monguno, ya yi zargin cewa wasu kudaden da aka ba tsoffin hafsoshin tsaro domin sayan makamai sun yi batan dabo.

A cewar Monguno, an bada kudaden ne domin sayen makamai don karfafa yakin ‘yan ta’addan Boko Haram.

Tsoffin hafososhin tsaron sune Janar Abayomi Olonisakin; Lt-Gen. Tukur Buratai, Vice Admiral Ibok Ekwe Ibas; Air Marshal Sadique Abubakar, dukka masu murabus.

Tuni Monguno ya ce anyi masa mummunan fassara ne ba haka yake nufi ba.Buratai ya bayyana cewa ko sau guda Monguno bai ambaci sunansa ba.

Sai dai a wani jawabi da ya fitar, Manjo Janar Babagana Monguno (mai ritaya) ya ce ‘yan jarida sun rikada kalamansa bayan hirar da ya yi da BBC Hausa.

Labarai Makamanta