Ban Amince Da Sakin Almajiran Zakzaky Da Kotu Ta Yi Ba – El Rufa’i

Gwamnatin jahar Kaduna a karkashin jagorancin gwamnan jahar, Malam Nasir Ahmad El-Rufai ta dauki alwashin kalaubalantar hukuncin kotun da ta saki ‘yan Shia 92 ta hanyar daukaka kara zuwa kotun daukaka kara.

Wata babbar kotun jahar Kaduna ce ta yanke hukuncin sakin ‘yan shi’an tare da wankesu daga tuhume tuhumen dake rataye a wuyansu bayan kwashe tsawon shekaru hudu a gidajen yari, bayan gwamnatin jahar ta kasa tabbatar da laifin mutanen, a cewar kotun.

Cikin wata sanarwa da babban lauyar jahar Kaduna, kuma kwamishinar sharia ta jahar, Aisha Dikko ta fitar, ta bayyana cewa gwamnati ba ta gamsu da hukuncin kotun ba, don haka za ta kalubalanci hukuncin a kotun gaba. “Ba mu gamsu da hukuncin kotun ba, muna kallon hukuncin a matsayin kuskure a doka, kuma babu wani kwakkwaran dalilin yanke wannan hukunci duba da tarin hujjojin da muka gabatar ma kotu a kan wadanda ake kara” Inji ta.

Gwamnatin Kaduna ta tuhumi ‘yan shi’an ne da laifukan da suka shafi tashin hankali, kuma tun 2015 ake tsare da su bayan kama su a Zariya lokacin rikicinsu da sojoji wanda ya yi sanadiyyar mutuwar daruruwan ‘yan kungiyar ta Shi’a mabiya Ibrahim el-Zakzaky.

Sai dai a na ta bangaren, kungiyar ‘yan Shi’an ta bayyana hukuncin kotun a matsayin nasara da tabbatar gaskiya da adalci, wanda kuma suke fatan zai zama sanadin sakin jagoransu.

Related posts