Ban Amince Da Hukuncin Kotu Ba – Tsohuwar Ministar Ruwa

Labarin dake shigo mana daga birnin Jos na Jihar Filato na bayyana cewar tsohuwar Ministan Albarkatun Ruwa zamanin mulkin tsohon shugaban kasa Jonathan Mrs Sarah Ochekpe ta ce bata gamsu ba da hukuncin da kotu ta yanke mata na daurin shekaru uku da wasu mutane biyu kan zargin cire kudi Naira miliyan 450.

Kotun ta yanke mata hukuncin ne tare da shugaban riƙon ƙwarya na jam’iyyar PDP na Jihar Plateau, Hon Raymond Dabo da Leo Jitung bisa dalilan cin amanar kasa.

Mrs Ochekpe, wacce ta yi martani kan hukuncin a St Jarlath Secondary School Bukuru, inda ta ke koyarwa ta ce ta bukaci lauyoyinta su yi nazarin hukuncin domin su bata shawarar matakin da za ta dauka.

Mrs Ochekpe ta ce EFCC ta gayyaci su zuwa ofishinta a Gombe a 2016, suka amsa gayyatar a Janairun 2017. Ta ce dukkansu ba su san dalilin da yasa aka gayyace su ba amma jami’an EFCC sun fada musu ana zarginsu ne da rike kudin sata da ya kai Naira miliyan N450.

“Mun rubuta takarda inda muka ce an yi zaben shugaban kasa da yan majalisar tarayya kuma an turo kudin ne daga Abuja zuwa Jihar Plateau. “An zabi mutum uku su karbi kudin a madadin PDP na Jihar Plateau, kuma muka karba kudin ba tare da sanin akwai wata matsala ba.

“An bukaci mu bada bayanin kudaden da suka shiga asusun mu na banki sai suka yi ikirarin cewa kudin sata ne muka ce musu ba mu da masaniya kan hakan.” Ta cigaba da cewa an dauko kudin daga banki kuma aka kai ofishin kamfen sannan mai ajiyan kudi ya tabbatar da hakan.

“Hakan yasa alkali ya wanke mu daga zargin. Amma aka fada mana cewa an same mu da laifin hadin baki kuma wai ba mu karba kudin ta hukumar da aka amince da rika hada-hadar kudi ba. “An ci kowannen mu tarar N1m, muka biya sannan muka tafi gida.

Mu dai ba mu gamsu da wannan hukuncin kuma mun fada wa lauyoyin mu kuma suna duba abin sannan su bamu shawarar abin da za mu yi,” in ji ta.

Labarai Makamanta

Leave a Reply