Bamu Makara Ba A Kokarin Tsamo ‘Yan Najeriya Miliyan 100 Daga Talauci – Buhari

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Mai girma Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce har yanzu tsarinsa na fitar da yan Nijeriya miliyan 100 daga kangin talauci cikin shekaru 10 zai yiwu, domin ba a makara ba.

Shugaban kasar ya bayyana hakan ne a ranar Lititin bayan kaddamar da Gonar Zamani a Suduje-Daura ta Hukumar Cigaban Kasar Noma ta Kasa, NALDA, a jihar Katsina.

Shugaba Buhari yana kyautata zaton za a iya cimma wannan buri duba da yadda gwamnati da mutane ke hadin gwiwa wurin habbaka tattalin arziki ta hanyar amfani da harkokin noma.

Shugaba Buhari, cikin sanarwar da kakakinsa Garba Shehu ya fitar ya ce dogaro kan man fetur ya janyo koma bayan tattalin arziki tsawon shekaru saboda rashin tabbas na farashin man fetur da ke shafan kasafin kudi da aiwatar da shi.

Shugaban kasar ya ce abin da ya fi zama tabbas ga yan Nijeriya shine noma, duba da cewar Nijeriya tana da yanayi mai kyau da kasar noma da kiwo tare da dimbin mutane da a shirye suke su koyi sabbin dabarun aikin noma.

“Ina son in jadada niyyata ta tsamo yan Nijeria miliyan 100 daga kangin talauci abu ne mai yiwuwa. Kasar mu na da yanayi mai kyau, kasan noma mai kyau da mutane da kayan aiki, tare da juriya da jajircewa irin ta matasa da ke son kawo sauyi a kasar.

“Za mu iya, kuma za mu yi. Babu wata hujja da za a iya bayarwa na cigaba da zama kasa da ke dogaro kan abu daya domin tafiyar da tattalin arzikinta duba da kalubalen sarrafa mai da hawa da saukan farashin mai a kasuwan duniya a yayin da muna da damar noma da kiwo.”

Labarai Makamanta