Bama Bukatar Shugaban Da Zai Murkushe ‘Yan Bindiga A Yanzu – Dr Gumi

Labarin dake shigo mana daga jihar Kaduna na bayyana cewar Shahararren Malamin Addinin Musuluncin nan Sheikh Ahmad Gumi, ya roki ‘yan Arewa kar su zabi ‘yan siyasar dake shirin murkushe ‘yan bindigan jeji.

Jaridar PM News ta ruwaito Malamin na cewa bai kamata a kashe ‘yan bindigan jeji ba, kuma ‘yan arewa na bukatar wanda zai yarda ya zauna da su a yi sulhu.

Fitaccen Malamin Addinin mazaunin jihar Kaduna ya yi wannan furucin ne a ɗaya daga cikin karatuttukan da ya saba gudanarwa a masallacin juma’a na Sultan Bello dake garin Kaduna.

“Cikin ‘yan takarar nan ina bin lafazinsu na ga lafazin waɗansu suna jiran wai kawai a basu mulki ne su kara makamai da za’a murkushe mayaƙanmu a cikin daji….mutanen mu a cikin daji.” “Alhali mu muna son a samu shugaban da zai zo a zauna da shi a fahimtar da shi, a kira mutanen nan a yi masu abinda ya kamata ai masu, don mu samu me? Zaman lafiya.”

Sheikh Gumi ya jima tsawon shekaru yana kira da a yi sulhu da ‘yan bindiga, waɗanda suka jefa mutane da yawa cikin matsin rayuwa ta hanyoyi da dama. Malamin yace kauna da kishin kasa, jiha da mutane baki ɗaya ya sanya yake son a zauna da ‘yan bindiga a yi sulhu.

Labarai Makamanta