Bala’in CORONA: Tilas Arzikin Najeriya Ya Karye – Ministar Kudi

Hasashe da bincike na tsimi da tanadi da hukumar kiddiga ta Nijeriya ta gudanar ya nuna tattalin arzikin Nijeriya zai shiga halin tabarbarewa da kashi -4.4 saboda annobar Coronavirus, kamar yadda Premium Times ta ruwaito

Ministar kudi, Zainab Ahmad ce ta bayyana haka ga manema labaru bayan kammala taron majalisar tattalin arzikin kasa daya gudana a ranar Alhamis.

Hukumar kididdig ta gudanar da bincike, kuma sakamakon binciken ya nuna tattalin arzikin Najeriya za ta shiga mawuyacin hali, za ta fadi da kashi -4.4.

Najeriya na cikin kasashen da suka fi fuskantar matsala sakamakon annobar Corona saboda babbar hanyar samun kudinta shi ne sayar da man fetir, wanda a yanzu darajarsa ta karye.

Related posts