Badakalar Kwangila: ‘Yan Majalisa Sun Kai Ruwa Rana

Rahotannin dake shigo mana daga Birnin tarayya Abuja na bayyana cewar batun yunkurin gyaran majalisar tarayya na naira na gugar naira har biliyan 42 ya janyo cece-kuce musamman daga ‘yan majalisar da kuma masu ruwa da tsaki.

Musamman idan aka kalli yadda za a iya amfani da naira biliyan 15 ko kuma kasa da hakan wurin aiwatar da gyaran bayan asalin maginan wurin sun kiyasta naira biliyan 26.9 a matsayin kudin da zai isa aikin.

Binciken ya bayyana yadda wasu ‘yan majalisa da dama suka nuna rashin amincewarsu da kwangilar da kuma irin dukiyar da aka ware don kwangilar, har da kuma rashin tabbaci akan kamfanin Messrs Visible Construction Limited, wanda aka ba damar aiwatar da kwangilar.

Labarai Makamanta