Badakala: EFCC Ta Gayyaci Hadimar Ministan Shari’a

Labarin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa hukumar yaki da rashawa ta EFCC ta yi wa Ladidi Mohammed, shugaban sashin kwato kadarorin gwamnati na ma’aikatar shari’ar tambayoyi kan zargin badaƙalar damfara.

Da farko, an tsare Ladidi, wacce ta hannun daman Abubakar Malami, ministan shari’a kuma antoni janar ne, na tsawon kwanaki kan zargin damfara wurin sayar da kayayyakin gwamnati na biliyoyin naira da aka kwato daga ‘barayin gwamnati.’

An bada belinta amma bata cika ka’idojin belin ba sai ranar Alhamis. Amma, majiyoyi sun tabbatar da cewa Ladidi ta koma ofishin hukumar a ranar Juma’a domin cigaba da amsa wasu tambayoyin.

An ruwaito cewa ta fada wa EFCC ta bi umurnin minista ne wurin sayar da kadarori da gwamnatin tarayya ta kwato hannun mutanen da ake zargi da rashawa. Sai dai bata iya gabatar da takarda da ke matsayin hujja a hakan ba.

Labarai Makamanta