Badakala: An Yi Wa Tsohon Gwamnan Zamfara Hisabi

Rahotannin daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar binciken da hukumar EFCC take yi ya bankado wasu akalla Dala $700, 000 da tsohon gwamnan jihar Zamfara Abdul-aziz Yari ya kashe daga cikin Naira biliyan 20 da ya karba wajen zuwa kasar Saudi Arabia.

Rahoton ya ce babban ‘dan siyasar ya karbi wadannan makudan kuɗaɗen ne daga wajen Akanta Janar ya tafi Umrah da su, Yari ya dauki hadimansa zuwa ketare inda aka kashe kudin.

Wani wanda ya san halin da ake ciki, ya shaidawa majiyar mu cewa wadannan kudi da aka wawura su na cikin 13% da ake warewa jihohin da ke da arzikin mai, A maimakon Akanta Janar Ahmed Idris ya biya wadannan jihohi tara hakkokinsu, sai ya ba Daraktan Westgate Projects Limited, Gbenga Akindele aikin Naira biliyan 84.

Wannan bincike na EFCC ya nuna Idris ya hada-kai da Yari, da wasu ma’aikatan hukumar kason albashi da arzikin kasa na RMAFC wajen karkatar da kudin.

Haka zalika babban Akantan na gwamnatin tarayya ya samu hadin-gwiwar wasu ma’aikata daga wadannan jihohi wajen yin kashe mu raba da sunan aiki. An yi kashe-mu-raba Shi wannan Akindele ya karbi N84bn na aikin bogi da ya yi, shi kuma ya shiga rabo.

Shi dai Yari ya karbi na sa kason ta hannun Anthony Yaro, wanda yake da alaka da Finex Professionals Services, ana tunanin Yari yake yi wa aiki.

Labarai Makamanta