Badaƙalar Makamai: Shugaban Dakarun Soji Ya Bayyana Gaban Majalisa

Rahotanni daga babban birnin tarayya Abuja sun bayyana cewa shugaban sojojin ƙasar nan, Janar Ibrahim Attahiru, ya bayyana a gaban kwamitin majalisa don amsa tambayoyi dangane da batun makamai da ake ta cece kuce akai.

Majalisar ta kafa kwamitin ne domin bincikar yanda aka siya, aka yi amfani da makamai da harsasai da sauran kayan yaƙi a rundunar sojoji da sauran hukumomin tsaro.

Kwamitin ya gayyaci shugaban sojojin aƙalla sau biyu domin yazo ya amsa tambayoyi kan yadda aka siya makaman da kuma yadda aka yi amfani da su. Hakanan kwamitin ya gayyaci gwamnan babban bankin Najeriya, Gowin Emefiele, da ya bayyana a gabansu domin amsa tambayoyin kan kuɗin makamai da aka ware.

Sai dai a ranar Jumu’a, kwamitin ya ɗage zaman har zuwa ranar Litinin bayan dogon jiran waɗanda aka gayyata ɗin ba su zo ba.

A kwanakin baya, ranar 22 ga watan Maris 2021, kwamitin ya gayyaci manyan mutanen biyu, gwamnan babban Banki da kuma Shugaban Dakarun Sojin.

Amma saboda rashin amsa gayyayar kwamitin da suka yi, ‘yan majlisun dake cikin kwamitin sun sake basu wa’adin su bayyana kafin 7 ga watan Afrilu.

Labarai Makamanta