Babu Yunwa A Najeriya – Ministan Yada Labarai

Rahoton dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Lai Mohammed, ministan yada labarai da al’adu, ya ce gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta cimma nasarar samar da abincin da kuma bunkasar kayyayakin da aka ‘kera a Najeriya.

Ministan ya bayyana haka ne a ranar alhamis a abuja a yayin wata ganawa da ya yi da manema labarai a Ofishin sa.

A cewar Mohammed, duk da rikice-rikicen da suka shafi tsadar rayuwa, gwamnati tayi kyakyawan aiki tun bayan hawanta kan karagar mulki a fannin dogaro da kai.

“Na tabbata da yawa da ga cikinmu sun ga bidiyon manyan kantunan da ba komai a cikinsu a kasahshen yammacin duniya, musamman a lokacin Covid-19. “Tun kafin wannan rikece-rikice shugaba Buhari ya sha gargadin ‘yan Nigeria da su noma abinda zasu ci daga daga abinda suka samar.

“Da yawa basu fahimci muhimmancin gargadin ba da kuma alfanunsa. To Sakamakon wannan Magana tasa, ‘yan Najeriya su ka shiga taitayinsu kuma hakan ya ceci Nigeria, musamman a lokacin da aka dad’e ana kullen korona da lokacin da k’asashen duniya suka daina fitar da kayyakinsu zuwa wasu k’asashen.”

A cewarsa, yawan takin da ake hadawa na zamani a kasar ya karu zuwa kashi 10, haka kuma an samu karuwar masana’antar sarrafa shinkafa da injinan ni’kanta, wanda ya taimaka wajen samar da wadataccen abinci.

“idan ka ziyarci kasuwannin mu da kantunanmu, abinda zaka gani galibi su ne kayayyakin da aka yi a Nigeria. Wannan babban ci gaba ne a kankanin lokaci.”

Labarai Makamanta