Babu Wata Ganawar Da Gwamnonin G5 Suka Yi Da Atiku – Gwamna Ortom

Labarin dake shigo mana daga Makurdi babban birnin Jihar Binuwai na bayyana cewar an yi watsi da ikirarin cewa gwamnonin da ke fushi da jam’iyyar PDP, sun yarda kuma sun amince su goyi bayan takarar dan takarar shugaban kasarta, Atiku Abubakar.

Samuel Ortom, gwamnan jihar Benue, cikin wata sanarwa da ya fitar ta bakin mashawarcinsa na musamman kan watsa labarai, Terver Akase, ya yi watsi da ikirarin a ranar Talata, 10 ga watan Janairu,

Gwamnonin da ke fushi da jam’iyyar PDP wadanda aka fi sani G-5 da suka hada da Ortom (Binuwai) Seyi Makinde (Oyo), Ifeanyi Ugwuanyi (Enugu), Nyesom Wike (Rivers) da Okezie Ikpeazu (Abia). Sun nisanta kansu daga kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na Atiku har sai an cika musu ka’idarsu na tsige Iyorchia Ayu, wanda shine shugaban jam’iyyar na kasa.

Akase ya bayyana rahoton a matsayin tatsuniya da aka kirkira da nufin kunyata gwamnonin na G5 da suka zabi neman ganin an musu adalci, gaskiya da daidaito a Jam’iyyar PDP.

Hadimin gwamnan ya bayyana cewa masu yada labarin kawai suna neman cimma wata manufa ce tasu ta siyasa, shi yasa suka gaza fadin inda gwamnonin suka hadu kuma suka cimma wannan shawarar.

“Marubutan suna son amfani da damar rikicin da ke faruwa a PDP din ne don cimma manufansu. Gwamna Ortom da wasu mambobin G5 ba su goyi bayan dan takarar shugaban kasar ba.”

Labarai Makamanta