Babu Wani Cigaba Da APC Ta Kawo A Najeriya – Darma

Tsohon shugaban hukumar Kula da asusun man fetur ta kasa wato (PTDF) kuma jigo a jam’iyyar adawa ta PDP a jihar Katsina, Injiniya Muttaqa Rabe Darma ya bayyana cewa, babu wani abun da jam’iyyar APC ta amfanawa ‘yan Nijeriya sai kawo zaman dar-dar da rashin tsaro da satar mutane da ya ki karewa.

Muttaqa Rabe ya bayyana haka ne a hedkwatar jam’iyyar PDP reshen jihar Katsina.

Injiniya Muttaqa ya kara da cewa “sakamakon irin farfagandar da APC ta yi a can baya shi ya haifar da dukkan wadannan matsaloli da suke ta kara faruwa.

Akwai lokacin da aka sace mutune arba’in da daya a Zamfara, ya fito ya ce, su maido musu shanun su, su maido mana mutanen ku.

“A da, da ni da ku babu wanda ya san satar jama’a har a je a yi cinikin su kamar wasu awaki, wadda jam’iyyar APC ne ta kawo mana shi.

A sace mutum a wannan mulki na APC ya Kai miliyoyin nairori sannan a sake shi, wanda ya zama ruwan dare a wannan lokacin.

Dukkan wadannan matsaloli idan ba mu tashi tsaye ba muka Kori jam’iyyar APC ba, wataran kana zaune gidanka barayin mutanen nan za su Kwankwasa ma gida a tafi da kai, sai an saida wannan gida naka a amso ka.

Kamar yadda ya fara faruwa a Gachi da ke Karamar hukumar Kankiya”

Muttaqa Rabe ya cigaba da cewa, korar APC a kowane mataki jihadi ne, domin magance wannan bala’i da ta kawo mana a cikin kasa.

Yanzu ba yunwa ke akwai ba, abinda ke yunwar nan misali jihar Katsina kudin da ake ba mu da na kasar baki daya ana sanya su ta wata hanyar da bai kamata ba.

Saboda hatta majalisar dinkin duniya ta tabbatar da cewa Nijeriya ita ce kasar da tafi kowacce kasa talauci a duniya.

Shi kuma talauci yana kawo ta’adanci, yunwa, shiga mata harkar karuwanci, malaman addini su yi karya domin a ba su wani abu, yana sa dan kauye ya shigo birni.

Daga karshe ya yi kira ga ‘yan Nijeriya su zabi jam’iyyar PDP a kowane mataki domin fitar da su daga cikin kangin talauci da yunwa da rashin tsaro da APC ta jefa al’ummar kasar nan a ciki.

Related posts