Babu Wanda Zai Tilasta Mata Yin Aure A Afghanistan – Taliban

Kungiyar Taliban ta fitar sabuwar doka da ta yi kira a ɗauki matakin da ya dace don tabbatar da ‘yancin mata a Afganistan.

Umurnin dokar ya ce kada a tilasta wa mata aure, sannan kuma ta yi bayani kan haƙƙin mallakar dukiya idan mijin mace ya mutu.

Amma babu maganar haƙƙin aiki ga mata ko kuma batun da ya shafi ilimi.

Haƙƙin mata ya zama abin damuwa tun lokacin da Taliban ta karɓi ikon Afghanistan a watan Agusta

Kusan an umarci mata su kasance a gida ba zuwa makaranta, kuma a watan da ya gabata an haramta wa mata fitowa a shirye shiryen talabijin.

Labarai Makamanta