Babu Wanda Ya Naɗa Sanusi Halifa – Tijjaniya

Cibiyar Dariqar Tijjaniya ta fito fili ta musanta ba tsohon Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II shugabancinta na Najeriya, kamar yadda labarin ya yi tambari a faɗin tarayyar Najeriya.

Sheikh Mahi Nyass, shugaban darikar Tijjaniya na duniya wanda ake kira da Khalifatum Arrm, ya bayyana hakan yayin da yayi jawabi ga manema labarai a Sokoto.

An ruwaito cewa, Nyass, wanda shine babban ɗa kuma magajin Shehu Ibrahim Nyass, yace in har za a yi naɗi ana tantancewa sannan a zaba daga cikin mabiyanta na Najeriya da Senegal.

Sheikh Nyass ya ƙara da cewar “Irin waɗannan hukunce-hukunce ana tattaunawa ne sannan a amince tsakanin masu ruwa da tsaki kafin a sanar.

Bayan an zabi mutum, akwai wasikar amincewa daga malamai wacce Khalifatul Arrm zai saka hannu kuma ya mika ga wanda aka nada,” Nyass yace.

Sheikh Nyass ya cigaba da cewar Sanusi bai nuna bukatar kujerar ba kuma shugabannin basu riga sun fitar da tsarin da za a bi ba wurin wannan nadin.

“Hadin kan ‘yan kungiya yana da amfani kuma ina kira ga kungiyar da ta mayar da hankali wurin bauta, kara dankon zumunci da kaunar juna,”.

Anashi ɓangaren Sheikh Ibrahim Dahiru-Bauchi, ya kwatanta labarin nadin Sanusi a matsayin labarin ƙanzon kurege da bai da tushe balle makama labarin bogi ne kawai.

Labarai Makamanta