Babu Surukuntaka Tsakanin Buhari Da Kumo – Fadar Shugaban Kasa

Mai magana da yawun shugaban ƙasa Malam Garba Shehu, ya ce Gimba Ya’u kumo da hukumar yaƙi da cin hanci ta ICPC ke nema ruwa a jallo yanzu ba surikin shugaba Buhari ba ne.

A cikin wata sanarwa da Garba Shehun ya fitar a ranar Jumma’a ya ce auren da ke tsakanin jami’in da ake zargin da ɗiyar shugaba Buhari ya jima da mutuwa.

Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito Garba Shehu na cewa koda ma auren bai mutu ba shugaba Buhari kamar yadda kowa ya san shi ba zai bayar da kariya ga duk wani mai laifi ba.

Tun a shekara ta 2016 ne dai aka ɗaura auren da ke tsakanin ɗiyar shugaba Buharin da kuma wanda ICPC ke nema. Sai dai Garba Shehu bai faɗi zahirin lokaci da shekarar da auren ya mutu ba.

ICPC dai na zargin Gimba Ya’u Kumo ne da zambar kuɗaɗen da suka kai Dala miliyan 65 kuma hukumar ta ce jami’in ya gudu.

Labarai Makamanta

Leave a Reply