Babu Sauran Sulhu Da ‘Yan Bindiga Sai Kisa – Masari

Labarin dake shigo mana daga Jihar Katsina na bayyana cewar Gwamnan Jihar Aminu Bello Masari ya yi fatali da maganar zaman sulhu da yan bindigan, waɗanda suka addabi jiharsa da sauran jihohin arewa ta yamma.

Masari ya bayyana matsayarsa ne yayin zantawa da kafar watsa labarai ta DW hausa, ranar Asabar.

Gwamnan ya maida martani ga wasikar dake yawo ta neman zaman sulhu, wanda gawurtaccen ɗan bindiga Bello Turji, ya aike wa gwamnati.

Gwamna Masari, wanda a baya gwamnatinsa ta rungumi tattaunawar sulhu, yace ba sauran tattaunawar sulhu tsakaninsu da yan bindiga a yanzu sai kisa kawai.

Masari ya bayyana cewa abin da wasikar Turji ta ƙunsa ba gaskiya bane. Gwamnan yace: “Sulhu da wa? Waye shi da yake neman sulhu ko a tsagaita wuta? Shi babban maƙaryaci ne, bai isa ya faɗa mana yadda za’a zauna lafiya ko sulhu ba.”

“Ƙaje ka samu iyalan waɗanda yan bindiga suka kashe, ku nemi sulhu da su, kuga yadda zata kaya. Kuma har da saka wasu sharuɗɗa, waye shi da zai kafa mana sharuɗɗa?” “Shi ke neman sulhu amma har yana da bakin kafa wasu sharudda da za’a cika.”

Tawagar Turji na ɗaya daga cikin kungiyoyin yan ta’adda da suka addabi yankin arewa maso yamma da wasu sassan arewa ta tsakiya.

Labarai Makamanta