Babu Ruwana Da Addini Idan Na Tashi Rusau – El Rufa’i

“Idan na tashi rusau babu ruwana da Masallaci ko Coci, don na rusa wasu a Abuja kuma ba abinda ya sameni”

Gwamnan jihar Kaduna Nasiru Ahmed El-rufa’i, ya mayar da martani ga masu yin ce-ce-ku-ce gami da Allah wadai kan rusau da yake yi da sunan gyara a jihar Kaduna.

Ya bayyana cewa babu ruwanshi da Masallaci ko Coci idan ya tashi rusau, don ya rushe wasu a Abuja ma, amma ba abinda ya same shi duk da wasu na addu’a da tsinuwa amma dayawa sun mutu su barshi lafiya.

Labarai Makamanta

Leave a Reply