Site icon Muryar 'Yanci – Labaru, Siyasa, Tsaro, Lafiya, Ilimi…

Babu Mutumin Kirki Ko Guda A Jam’iyyar APC – Sule Lamido

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar tsohon gwamnan jihar Jigawa kuma jigo a jam’iyyar PDP, Sule Lamido, ya caccaki ayyukan jam’iyyar APC a kasar nan, inda ya bayyana su a matsayin bigi bagiro.

Yayin da yake bayyana ayyukan gwamnatin APC kawo yanzu, Lamido ya bayyana jam’iyya mai mulki a matsayin jam’iyya juya wacce ba ta iya samar da kyakkyawan shugabanci ga kasar nan ba a tsawon lokaci da ta ɗauka akan mulki.

Sule Lamido ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da yayi da manema labarai ranar Talata, a birnin tarayya Abuja.

Lamiɗo ya yi nuni da cewa jam’iyyar mai mulki ita ce ke tafiyar da mulki amma ba ta da karfin kawo canjin da ‘yan Najeriya ke bukata, ta gaza ta kowane fanni.

“Abin da su (APC) suke cewa PDP kazanta ce amma suna farautar mambobinmu su zo su gina jam’iyyarsu. APC da ke daukar ‘ya’yan PDP zuwa cikinsu cin rashawa ne. “Babu nagari a APC. Jam’iyyar ta rashawa ce matuka.”

Da yake magana kan taron gangamin jam’iyyar PDP da aka kammala da kuma damar da jam’iyyar za ta samu a zaben 2023, Lamido ya bayyana fatan samun nasara ga jam’iyyarsa, inda ya kara da cewa sakamakon taron na nuna hangen ci gaba ga kasar.

Exit mobile version