Babu Inda Ya Kai Arewa Daɗin Zama – Ƙungiyar Cigaban Inyamurai

Kungiyar kare hakkin kabilar Inyamurai ta kasa Ohanaeze Ndigbo, ta siffanta Arewacin Najeriya a matsayin wurin da ‘yan kabilarsu suka fi samun kwanciyar hankalin rayuwa da kasuwanci a fadin Najeriya.

Shugaban kungiyar na shiyar jihohin Arewa 19, Augustine Amaechi, a ranar Juma’a a Abuja ya bayyana cewa Arewa ta ba Inyamurai masauki fiye da yadda ake tsammani, idan aka kwatanta da sauran yankunan ƙasar.

Amaechi ya ce akan samu saɓani wasu lokuta saboda a rayuwa dole a samu hakan, amma a magana ta gaskiya babu inda ya kai Arewa daɗin zama da kwanciyar hankali ga Inyamurai.

A kan maganar ballewar da Inyamurai ke yunkuri yi daga Najeriya, ya ce rashin ayyukan yi ya sabbaba hakan. Ya kara da cewa tun da Inyamurai sun shahara da kasuwanci, suna bukatan Arewa domin tara arziki.

“Magabatanmu na cewa duk da cewa matasanmu sun fusata, muna bukatar garambawul a kasar nan ba ballewa ba saboda ba zaka iya sayar da kayanka a kauyenka ba,”.

Anashi ɓangaren Shugaban kungiyar Ohanaeze Ndigbo na kasa, George Obiozor, ya ce al’ummar Inyamurai ba su yaki da kowa. “Abinda muke so kawai shine daidaito da sauran jama’a. Lokaci ya yi da zamu fadawa shugabanni gaskiya,”.

Labarai Makamanta