Babu Inda Nace Ina Neman Mijin Aure – Jaruma Zakiyya Abdullahi


Tsohuwar jaruma Finafinan Hausa Zakiyya Ibrahim Abdullahi, ta yi kira ga ‘Yan jarida da su rinka gudanar da aikin su a bisa doron aikin jarida, a matsayin su na wadanda Allah ya dora musu nauyin fadakar da jama’a da wayar musu da kai, a kan abubuwan da su ke faruwa a duniya.

Jarumar ta yi wannan kiran ne, a lokacin da ta ke hira da wakilin jaridar Dimokuradiyya, a kan labarin da wata jarida mai suna Damagaram Post ta yi, in da ta ce, wai tana neman mijin aure.

Jarumar ta Kara da cewar ” Sam babu wani lokaci da na taba yin hira da wani dan jarida na fada masa ina neman mijin aure, saboda haka ban san a ina suka samo labarin na su ba, kuma suka alakanta ni da shi.” Inji ta.

 ” Idan ina neman mijin aure ba zuwa Soshiyal Midiya zan yi ba na rinka tallan kaina ba, kuma idan tallan kai ne ai mu a matsayin mu na ‘yan fim duniya ta gama sanin mu. Don haka labarin da suka yada ba gaskiya ba ne, don har na so na dauki mataki na shari’a a kan su, saboda bata mini sunan da suka yi.

Labarai Makamanta