Babu Inda Nace Ayyana ‘Yan Bindiga Matsayin ‘Yan Ta’adda Zai Tarwatsa Najeriya – Gumi

Labarin dake shigo mana daga Jihar Kaduna na bayyana cewar Shahararren malamin addinin musuluncin nan, Sheikh Ahmad Abubakar Gumi, yace ana jingina masa maganganun da bai yi ba, ta hanyar ƙage da sharri akan ‘yan Bindiga domin kawai a ɓata mishi suna.

Shehin malamin ya musanta maganar da ake jingina masa cewa wai ayyana yan bindiga a matsayin yan bindiga zai kawo karshen Najeriya. Malamin ya bayyana cewa sam bai faɗi haka ba, mutane ne ba su fahimnci abinda yake nufi ba.

Gumi ya faɗi haka ne yayin da yake zantawa da manema labarai yayin ziyarar gani da ido a cibiyar Sheikh Uthman Bin Fodio a Kauyen Kahoto, wanda gidauniyar Sultan Bello ta gina wa makiyaya.

Sheikh Gumi yace kashi 99% na fulani makiyaya ba su da hannu a ayyukan yan bindiga, kuma idan aka ayyana makiyaya a matsayin yan ta’adda za’a samu matsala.

“Kashi 99 cikin dari na mutanen nan ba su da hannu a aikata ayyukan yan bindiga, idan aka ayyana su a matsayin yan ta’adda, Najeriya zata shiga matsala ta ko ina.” “Me kuma ya yi saura idan aka cewa kowane ɓangaren Najeriya yana ci da wuta? Idan aka sake makiyaya suka shiga rikicin addini, kasar nan zata shiga tasku.”.

Shehin malamin ya shawarci gwamnatin tarayya, maimakon kokarin kashe biliyoyin kudi wajen siyo makamai, kamata yayi ta gina makarantu. Ya kara da cewa ya zanta da tawagar yan bindiga da dama kuma sun tabbatar masa da cewa a shirye suke su aje makamansu su rungumi ilimi.

Da yake magana kan makarantar, Gumi yace cibiyar tana kunshe da azuzuwan karatu 6, wanda za’a cigaba da bada karatu awa 24 a kullum. “Makiyaya zasu fita kiwon dabbobinsu da safe, idan kuma sun dawo da yamma su halarci wurin ɗaukar karatu.”

“A halin yanzu zamu fara karatun Firamare da Sakandire. Muna da Asibiti a cibiyar, kuma za’a koya musu yadda zasu kara zamanantar da kiwon dabbobinsu.”

Labarai Makamanta